Ana nuna damuwa kan cikin-shege

Taswirar Najeriya
Image caption Ana kokawa kan yawaitar cikin-shege a Najeriya

Gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya, na nuna damuwa a bisa yawaitar yara jarirai da a kan haifa sakamakon cikin shege.

Hukumomin sun ce mata masu karancin shekaru,musamman 'yan makarantun sakandare ke haihuwar wadannan jarirai.

Malam Kabir Ishaq, shugaban gidan marayu ne a Zariya, kuma ya shaidawa BBC cewa:''Maimakon da ana yar da su(jariran) a bola,to yanzu ana kawo mana nan.Inda a ke samun matsala shi ne 'yan makarantar sakandare''.

Hukumomi sun yi kira ga iyaye su tarbiyantar da 'yayansu,don gujewa yawaitar cikin shege.