Najeriya: jiya ba yau ba

Cif Matthew Tawo Mbu
Image caption Cif Matthew Tawo Mbu tsohon ministan tsaron Najeriya

"A daidai lokacin da dare ya raba, sai suka mike suna kallon yadda aka saukar da tutar Burtaniya tare da sanya tutar Najeriya, abinda kuma ya kawo karshen shekaru 100 da Turawan Burtaniya suka shafe suna mulkar kasar. Kasa mai cike da tabbaci da hadin kai ta kafu a yau......"

Wadannan su ne kalaman da aka buga a ranar 1 ga watan Oktoba 1960 a jaridar Daily Times. Wani sharhi ne mai sosa rai da Babatunde Jose, editan jaridar na wancan lokaci ya rubuta.

Jaridar Daily Times, wacce aka kafa a shekarun 1920, ita ce mafi dadewa da kuma a kasar a wancan lokaci. Mr Jose, wanda ya fara aiki a matsayin dan koyo tun yana dan shekara 16, daga baya ya zamo wanda akewa lakabi "kakan aikin jarida a Najeriya", ya yabawa sabbin shugabannin kasar bisa kokarinsu na kafa tsarin dimokradiyya da bin doka da oda.

Ya bayyana cewa da an bar kundin tsarin mulkin shekarar 1960, da kasar ta zauna cikin kwanciyar hankali ba tare da cin zarafin bil'adama ba.

Mr Jose ya mutu a shekara ta 2008, yana dan shekara 82, ba tare da burinsa ya cika ba.

Matthew Tawo Mbu, dan shekaru 80, wanda tsohon ministan tsaro ne a lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai, ya tuna cewa shi da abokansa sun yi kwana suna biki har wayewar gari.

Bakin ciki da takaici

Mutuwar jaridar Daily Times a hannun gwamnatoci daban daban na kasar, ya bayyana yadda kasar ta shiga cikin rudanin shugabanci, wanda kuma yayi tasiri kan kusan kowanne sassa na ci gaban tattalin arziki a kasar.

Fata na gari

Duk da cewa man fetur shi ne ya zamo abin cece-kuce a Najeriya.

Sai dai akwai abubuwa da dama da kasar za ta bugi kirji da su.

A daidai lokacin da Daily Times ta fadi, a yau kasar ta samu kafafen yada labarai da dama wadanda kuma suke samun damar fadar albarkacin bakinsu.

Baya ga wannan akwai ci gaba a bangaren kamfanoni kamar na sadarwa da sufuri, kuma yadda gwamnati ta sha alwashin sayar da kamfanin wutar lantarki na kasar na nuna yadda abubuwa suka tabarbare.

A bangaren yaki da cinhanci da rashawa, a kwanakinnan aka kori shugabannin kasuwar hada-hadar hannaye jari ta kasar, sannan aka ce za su fuskanci shari'a.

Wasu na ganin kasar ta taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a kasashe irinsu Sierra Leone da Labaria da kuma yaki banbancin launin fata a Afrika ta Kudu.

Sai dai wasu na ganin, in banda kasancewa kasa daya tilo, akwai abubuwa da dama da yakamata kasar ta cimma a shekaru hamsin din data shafe a raye.

Karin bayani