Najeriya: Tuna baya shi ne roko

John Smith
Image caption John Smith a cikin abokansa lokacin yana Arewacin Najeriya

Mista John Smith na daya daga cikin 'yan mazan jiya da suka yi saura daga cikin Turawan mulkin mallaka da suka shugabanci Najeriya kafin samun 'yancin kai.

Duk da cewa rayuwarsa a Najeriya kamar tsintar kansa ne a wata duniya daban, ya ce ya kasance kamar a gida yake.

"Shekaru 20 din da na shafe a Najeriya su nafi jin dadinsu a rayuwata," a cewarsa. " ba wani abu dana kara yi wanda ya yi daidai da su."

Kakkyawar alaka

Mista Smith, dan shekaru 82, yana cikin daidaikun Turawan da suka yi saura wadanda suka mulki Najeriya kafin 1960. A yanzu ya dawo domin ganin irin yadda kasar take shekaru hamsin bayan samun 'yancin kai - tare da sabunta kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da jama'ar kasar.

Mista Smith ya hadu da Malam Sulaiman Baffa lokacin da yake horar da matasan Najeriya domin karbar ragamar ayyuka daga hannun Turawan Burtaniya.

Ya yaba da Malam Sulaiman- wanda shugaban makarantar Firamare ne a lokacin, abinda yasa yaja hankalinsa domin ya shiga aikin gwamnati.

Image caption 'Yan Najeriya na shirin gudanar da bikin samun 'yancin kai

Malam Sulaiman ya tuna cewa "manufar ita ce a bamu horo domin mu karbi ragamar ayyuka daga hannun Turawan mulkin mallaka. Kuma duk abinda muka koya mun koye shi ne ta dalilin Turawan Burtaniya, wadanda suka nuna mana mahimmancin juriya da kokari.

Ya kara da cewa "kuma duk abinda na yi a rayuwata, na yi shi ne abisa wannan tsari."

Tun daga wannan lokaci ne mutanen biyu suka ci gaba da alaka har yauzu.

"Ba abinda zan iya bayyana mista Smith da shi illa kawai na kira shi mai gidana," a cewar Malam Baffa - "kasancewarsa mutumin da ya taimakamin a rayuwa kuma kodayaushe yake nuna yarda da kwarin guiwa a kaina.

Dangantakar mutanen biyu ta nuna yadda alaka ta kasance mai tsauri kuma a wasu lokutan mai armashi tsakanin Turawan Burtaniya da jama'ar Arewacin Najeriya gab da samun 'yancin kan kasar.

Takaici

Fatan samun wata kasa mai cike da albarka shi ne cike a zukatan 'yan kasar, wacce tafi kowacce yawan jama'a a Afrika, ga dinbin arzikin man da ake shirin fara hakowa.

Sai dai juyin mulkin sojoji daban daban ya biyo baya kusan shekaru shida da samun 'yancin kai. Jim kadan bayan haka kuma sai kasar ta fada cikin yakin basasa, lokacin da jama'ar yankin Kudu maso gabas suka nemi kafa kasar Biafra.

Sannan kuma aka barnatar da kusan mafi yawan arzikin da ake samu daga danyan mai. An kiyasta cewa an sace akalla dala biliyan 400 daga baitul mailin kasar a shekaru 40 na farko.

An maido da tsarin mulkin farar hula a shekarar 1999, sai dai jama'a da dama na ganin akwai sauran tafiya a gaban kasar.

Malam Baffa bai so ya soki Najeriya ba, amma ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ya karu bayan Turawan Burtaniya sun fice daga kasar.

Image caption John Smith lokacin da yake rayuwa a Najeriya

An debi sababbin ma'aikata, wadanda basu samu horon da na baya suka samu ba.

Mista Smith yana kaunar Najeriya sosai ba kamar sauran takwarorinsa ba, ya ci gaba da zama a kasar yana aiki har shekara 9, bayan samun 'yancin kai.

Sai dai yace mulkin mallaka na da nasa matsalolin: "lokacin da Turawa suka zo Najeriya ba Sarauniya Elizabeth II bace jagora, kasar na karkashin Henry VIII, kuma mika mulkli a irin wannan yanayi kan dauki shekaru aru-aru, maimakon shekaru 60 da yi a Najeriya.

"Aikin mu a wancan lokaci shi ne mu tabbatar cewa Najeriya ta shiga cikin sauran kasashen duniya, wanda kuma muka yi ba tare da cikakkun kayan aikin da muke bukata ba," a cewar Mista Smith.

Ya kara da cewa shekaru 60 ba su da yawan da za a aiwatar da abubuwa masu yawa.

Karin bayani