Faransa ta gaskata hotunan 'yan kasar

Shugaban Faransa,Nicholas Sarkozy
Image caption Faransa ta gaskata hotunan 'yan kasar

Faransa ta ce hotunan 'yan kasarta su bakwai da gidan talabijin na Aljazeera ya nuna, wadanda kungiyar Al-Qaeda ta sace a Jamhuriyar Nijar makwanni biyu da suka gabata hotunan gaske ne.

Faransan ta ce hakan ya bata wani kwarin gwiwa kasacewa mutanen na nan da ransu, koda ya ke bata bayyana ko yaushe ne aka dauki hotunan ba.

Gidan talbijin na Al Jazeera ya nuna hotunan mutanen da aka sace wadanda biyar daga cikinsu 'yan kasar Faransa ne.

Dukkanin mutanen dai idan banda mutum daya, na aiki ne a wani kamfanin makamashin nukiliya na kasar Faransa, Areva, dake hakar ma'adinan Uranium a jamhuriyar Nijar.