Amurka ta nemi gafarar Guatemala game da ciwon tunjere

Amurka ta nemi afuwa saboda sakawa daruruwan mutane a Guatemala ciwo sanyi na gonorrhoea da tunjere, wato Syphilis lokacin wani gwaji magani shekaru sittin da suka gabata.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka , Hillary Clinton ta ce wannan gwaji da aka yi bai da ce ba kuma abin kyama ne.

Wata masaniyar kimiyyar siyasa Susan Reverby ce ta gano cewa yawancin wadanda wannan abu ya shafi marasa lafiya ne masu tabin hankali da kuma 'yan fursuna kuma an yi gwajin ne ba tare da amincewar su ba.

A lokacin Amurka ta so yin gwajin maganin Penicillin a matsayin riga kafi. Wakilin BBC ya ce ba a dai sani ko ya Allah maganin da aka yiwa wadanda abun ya shafa bayan gwajin ya wadata ba, ko kuma a'a.