Ra'ayi Riga: Shekaru hamsin da samun yancin kan Najeriya

Harin da aka kai da bam a Abuja
Image caption Harin da aka kai da bam a Abuja

A shekarar 1914 ne karkashin Jagorancin Gwamna Janar Fredrick Lugard aka hade yankunan arewa da kudu, karkashin kasa daya, wadda aka sanyawa suna Nigeria.

Turawan mulkin mallaka sun ci gaba da mulkin kasar inda a yankin kudu, suke mulki kai tsaye yayin da a yankin arewaci kuma suka gudanar da mulki ta hannun masarautun gargajiya.

Bayan an yi ta kai kawo a kan lokacin da ya dace a mika mulki, a karshe an amince da baiwa Nigeria'r 'yan cin kanta ranar daya ga watan Octoba na shekarar 1960.

Wadanda suka ganewa idanunsu yadda aka gudanar da mulkin mallaka gabanin samun 'yancin kan na bayyana cewar lamarin babu kyawun gani.

To a yau dai an gudanar da bukukuwa a sassa daban daban na Nigeria'r domin murnar cika shekaru hamsin da samun yan cin kan, ciki kuwa har da Abuja babban birnin Tarayyar Kasar.

Sai dai kuma a lokacin da ake gudanar da wanann buki, wasu nakiyoyi sun fashe a Abujar. Wadannan bama-bamai sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla takwas, yayin da wasu masu yawa suka samu raunika.

Kungiyar nan mai fafutukar kwato wa mutanen yankin Niger-Delta mai arzikin Man Petur hakkokinsu, ta MEND, ta dauki alhakin kai wannan hari, tana mai cewar ba ta ga wani abun yin bukukuwa ba a wanann lokaci.

To ra'ayi dai ya banbanta akan halin da Najeriyar ke ciki, bayan cika shekaru hamsin da samun mulkin kan.

Yayin da wasu ke cewar kasar ta samu ci gaba, wasu kuwa suna cewa ne ba su ga wani ci gaba da kasar ta samu ba a tsawon wannan lokaci.

To domin tattaunawa a shirin-namu na Ra'ayi Riga a yau, muna tare da Alhaji Yusuf Maitama Sule, Dan Masanin Kano, Kuma minista a Jamhuriyar ta farko karkashin jagorancin Pirayim Minista, marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa.

Haka nan kuma muna tare da Alhaji Adamu Ciroma, tsohon gwamnan babban bankin Nigeria, tsohon ministan harkokin kudi, kuma mutumin da suka yi takara tare da Dan masanin kano ta neman Jam'iyyar NPN, ta tsayar da daya daga cikinsu a matsayin dan takarar shugabancin kasa, tare da Alhaji Shehu Shagari, inda a karshe, suka sha kaye a hannun tsohon Shugaban Nigeria, Alhaji Shehu Shagari.

Haka nan kuma akwai mu da Minista mai ci yanzu a ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Nigeria, Dr Aliyu Idi Hong, Sai kuma Professor Sa'ad Abubakar, wani masanin tarihi da ke Jami'ar Abuja.

Akwai kuma wasu daga cikinku masu saurarenmu, ta wayar tarho.