Ana ci gaba da zanga-zanga a Faransa

Masu zanga-zanga a Faransa
Image caption Masu zanga-zanga a Faransa

Dubunnan daruruwan mutane ne a fadin kasar Faransa ke ci gaba da zanga-zangar kin kudirin Shugaba Nicholas Sarkozy na dage shekarun ajiye aiki wanda za a gabatar gaban majalisar dokoki ranar Talata mai zuwa.

An dai shirya zanga-zanga fiye da dari biyu a fadin kasar kuma wannan ce rana ta uku ta jerin gwanon da ake yi domin nuna rashin amincewa da sauye-sauyen da shugaban ya bayyana a watan jiya.

Wani daga cikin masu zanga-zangar a garin Toulouse, Jean Claude, ya ce suna gudanar da jerin gwanon ne cikin lumana domin kare ’yancinsu.

“Lokacin yunkurin hana wani abu bai taba kurewa ba.

“Muna gudanar da gangamin ne bisa turbar dimokradiyya cikin lumana.

“Kalli adadin mutanen da suka fito ciki har da wadanda ba su taba zanga-zanga a rayuwarsu ba”, inji Mista Claude.