Tarayyar Afirka ta yi tir da harin Abuja

Wasu daga cikin motocin da bama-bamai suka lalata a Abuja
Image caption Wasu daga cikin motocin da bama-bamai suka lalata a Abuja

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi tofin Ala-tsine a kan hare-haren bama-baman da aka kai ranar Juma'a a Abuja babban birnin Najeriya.

Shugaban gamayyar, Jean Ping, ya bayyana fatan za a kama wadanda suka kai harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Mista Ping na daga cikin manyan bakin kasashen ketare da ke halartar bukukuwan cikar Najeriyar shekaru hamsin da samun ’yancin kai lokacin da bama-baman su ka tashi.

Bama-baman dai da aka dasa cikin motoci guda biyu sun hallaka mutane goma sha biyu kuma wata kungiyar ’yan ta'adda da ke yankin Naija Delta, MEND, ta ce ita ta kai harin don nuna rashin gamsuwa da bukukuwan da ake yi.