Kungiyoyi sun yi gangami a birnin Washington

Shugaba Barack Obama na Amurka
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Daruruwan kungiyoyi ne suka taru a yau a birnin Washington domin gudanar da gangamin neman samar da aikin yi a Amurka.

Gangamin mai taken "Al'umma daya mai aiki a tare", ta hada da dubunnan mutane da suka kunshi kungiyoyin kwadago, da masu neman hakkin bil-Adama, da kuma kungiyoyin addinai.

Ana gangamin ne a matattakalar cibiyar tunawa da marigayi shugaba Lincoln, inda makonni biyar da suka gabata masu ra'ayin mazan jiya suka gudanar da wani gagarumin gangami.

Manazarta dai na cewa kungiyoyin da suka shirya wannan gangamin na fatan janyo hankalin mahukunta ne daga bukatar masu ra'ayin mazan jiya karkashin tutar Tea Party movement da ke ta gangami a fadin Amurka domin bukatar a rage haraji.