Amurka ta bukaci Pakistan ta binciki hoton bidiyo

Sojin kasar Pakistan
Image caption Wani hoton bidiyo dake nuna sojin pakistan suna harbin wasu gungun mutane ya ja hankalin gwamnatin Amurka.

Amurka ta bukaci gwamnatin Pakistan tayi bincike dangane da wani hoton bidiyo dake nuna sojan Pakistan suna harbe gungun wasu mutane dake daure ta hannu da fuska.

Ba 'a dai san daga inda wannan hoton bidiyon ya fito ba

Hoton bidiyon dai na nuna wasu muntane ne sanye da kakin soja suna shiga cikin daji da wasu mutane shida da aka rufewa fuska.