Salva Kiir ya ce ba dalilin hadewar Sudan

Shugaban kudancin Sudan, Salva Kiir
Image caption Shugaban kudancin Sudan, Salva Kiir

Shugaban kudancin Sudan, Salva Kiir, ya ce bai ga dalilin da zai zabi ci gaba da zaman Sudan kasa daya ba a zaben jin ra'ayin jama'a kan makomar kasar da za a gudanar a watan Janairun badi.

Sai dai wani na hannun damansa ya ce wannan ba yana nufin cewa zai zabi a raba kasar gida biyu ba ne.

Yarjejeniyar zaman lafiyar da kungiyarsa ta SPLM ta kulla da gwamnatin Sudan dai ta bukaceta da ta goyi bayan kasancewar Sudan kasa guda a zaben jin ra'ayin jama'ar da za a yi.

Kusantowar kada kuri'ar jin ra'ayin jama'ar dai lokaci ne da ke cike da taraddadi a Sudan.

’Yan Sudan da dama da kuma manazarta na kasashen waje na cewa akwai yiwuwar kasar ta sake afkawa kangin yakin basasa.

Mafi yawan man fetur din kasar dai yana kudu, don haka gwamnatin Khartoum ba ta so kasar ta rabe biyu.