Ana gudanar da zaben shugabankasa a Bosnia

Hotunan wasu 'yan takara a Bosnia
Image caption Al'ummar kasar Bosnia na gudanar da zaben shugabankasa da kuma 'yan majalisar dokoki

Al'ummar Bosnia na zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki, kuma wannan zabe bisa ga dukkan alamu zai tado da bambance-bambancen dake tsakanin Sabiyawa, da Crociawa da kuma musulmin kasar.

Bambance-bambancen tsakanin al'ummar Bosnia dai ya haifar da wani tsarin gwamnati mai sarkakiya.

Jama'ar kasar dai zasu so a bunkasa tattalin arzikin kasar ne, amma bisa ga dukkan alamu bambancin siyasa mai zurfin gaske a kasar ta Bosnia na kawo cikas ga samuwar hakan.