Ana zaben shugaban kasa a Brazil

Yau al'umar Brazil ke kada kuri'a domin zaben wanda zai gaji shugaban kasarsu mai ci, Luiz Inacio da Silva, wanda zai sauka bayan yayi wa'adin mulki biyu.

Abokiyar aikinsa ta jam'iyyar 'yan kwadago ta Workers Party, Dilma Rousseff, na fatan samun nasara a zagayen farko na zaben.

Babban wanda ke fafatawa da ita shi ne Jose Serra na jam'iyyar SDP ta Brazil, wanda shugaba Lula ya kayar a zaben 2002.