Za'a yi bukukuwan bude gasar Commonwealth a Delhi

Gasar wasannin kasashen commonwealth a birnin Delhi
Image caption A yau ake saran gudanar da bukukuwan bude gasar wasannin kasashen commonwealth a birnin Delhi na kasar India

Bayan an shafe makonni ana ta cece-kuce dangane da yanayin masaukin 'yan wasa, yanzu haka dai an kai ga matakin karshe na bude gasar wasannin kasashen kungiyar Commonwealth nan gaba yau a birnin Delhi na kasar India

Makawa da masu raye raye dubu bakwai ne zasu cashe a lokacin bukin bude gasar na tsawon sa'oi biyu, yayin da shi kuma Yarima Charles zai karanta jawabin sarauniya.

Hukumomin kasar ta India dai sun ce, sun tanadi 'yan sanda da masu aikin samar da tsaro na sa-kai kusan dubu dari domin bada tsaro ga 'yan wasa, da jami'an wasannin da ma 'yan kallo.