Kotun Isra'ila ta sami sojoji da laifi kan Falasdinawa

Wata kotun soja a Isra'ila ta samu wasu sojoji biyu da laifin yin amfani da wasu Falasdinawa fararen hula a matsayin garkuwa daga hare-hare a lokacin da suke kai farmaki a Gaza cikin watan Janairun bara.

Kotun ta ce abin da sojojin suka aikata sa bai dace ba, sun kuma wuce gona da iri, bayan da suka sa wani yuaro dan shekara goma sha daya, ya bincika wasu jakunkuna da ake zaton akwai bamabamai a cikinsu. Rahotani na nuna cewa wannan ne karon farko da aka samu wasu da laifi, kan wannan dabi'a da aka haramta, ta tilasta ma fararen hula yin wasu aikace aikacen da ya sojoji ya kamata su yi , amma suka amfani da su a matsayin garkuwa.