An bude gasar wasannin Kwamanwelz

An bude gasar wasannin kasashen Kwamanwelz, a Delhi, babban birnin kasar Indiya.

Da ma dai wadanda suka shirya gasar wasannin sun yi alkawari za a gabatar da kade kade da raye raye masu kayatarwa wadanda zasu nuna irin al'adu daban daban da aka san kasar Indiya da su.

Ana gudanar da bukukuwan ne a babban filin wasan da aka dauki tsauraran matakan tsaro a kewayensa.

Wannan ita ce zata kasance gasar wasannin kwamanwelz mafi girma a tarihi, kuma a gasar da ta fi kowace girma da yawan jama'a a cikin kungiyar.