Goodluck Jonathan ya ce 'yan ta'adda ne suka kai hari Abuja

Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya ya ce wata karamar kungiya ta 'yan ta'adda a wajen Nijeriya ce ta kai hare-haren bam din nan na shekaranjiya Juma'a, wanda ya halaka mutane akalla goma sha biyu, a lokacin bikin ranar zagayowar samun mulkin kan Nijeriya a birnin Abuja.

Shugaba Jonathan dai bai bayyana sunan kungiyar ba, amma ya ce wasu ne a cikin Nijeriya ke daukar dawainiyarta.

Tun da farko dai kungiyar 'yan gwagwaramayar yankkin Niger Delta ta MEND ta ce ita ta kai hare-haren, inda ta kara da cewar sai da ta sanar da hukumomin Nijeriyar kwanaki biyar kafin hare-haren, tana mai cewar sakacin jami'an tsaro ne ya janyo asarar rayuka.