Za a kyautata tsaron AREVA a Nijar

A jamhuriyar Niger hukumomin kasar da kamfanin AREVA na kasar Faransa mai gudanar da ayyukan hakar ma'adinin Uranium a Niger din sun kafa wani kwamitin hadin gwiwa domin tunkarar matsalar tsaro a harabar gidajen kwanan ma'aikata, da kuma tashoshin hakar karfen Uranium a Yankin arewacin kasar.

Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan wata ziyarar ganewa ido ne da shugabar kamfanin AREVA din Mrs Anne Louvergeon ta yi a Nijar, a makon jiya.

Hakan ya biyo bayan sace wasu 'yan asalin kasar ta Faransa su biyar da wasu 'yan Afrika biyu, wanda ake kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Al'qaeda a yankin Maghrib ne suka yi cikin watan jiya, a garin Arlit na jihar Agadez.