Malaman jami'a na yajin aiki a kasar Ghana

John Atta-Mills, shugaban Ghana
Bayanan hoto,

John Atta-Mills, shugaban Ghana

A kasar Ghana, malaman jami'o'i sun fara wani yajin aiki na sai illa masha Allahu.

A karshen makon jiya ne malaman jami'o'in suka fara kauracewa azuzuwa, domin matsawa gwamnati lamba, don ta biya su cikon karin albashin da tayi masu a shekarar da ta wuce.

A karkashin sabon tsarin albashin, kowane malamin jami'a zai rika karbar sabon kudin Cedi 1500 a kowane wata, wanda ke daidai da dalar Amurka 1500.

Gwamnatin Ghanar ta ce bata da kudaden biyawa malaman wannan bukata a halin yanzu, to amma bangarorin biyu na cigaba da sasantawa.