Okah ya gurfana a kotu kan harin Abuja

Mr Henry Okah, tsohon jagoran kungiyar MEND
Image caption Mr Henry Okah, tsohon jagoran kungiyar MEND

Wani dan Nigeria ya bayyana a gaban kotu a Africa ta Kudu, bisa zargin hannu a hare haren bam da aka kai a Abuja ranar juma'ar da ta gabata. An kama Mr Henry Okah ne ranar Asabar da safe, bisa tuhumarsa da laifuffuka masu nasaba da ta'addanci.

A ranar Juma'a ne, mutane kimanin sha biyu suka rasa rayukansu, bayan da wasu bama bamai da aka dana a wasu motoci biyu suka fashe a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan cika shekaru hamsin da samun 'yancin kai.

Wani bangare na kungiyar MEND ta masu gwagwarmayar 'yancin Niger Delta dai ya yi ikirarin kai wannan hari.