Shugaban Najeriya ya nada sabon mashawarci ta fuskar tsaro

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya nada sabon mashawarci na kasa ta fuskar tsaro.

Wanda aka nada shine Janar Andrew Azazi mai ritaya.

Zai maye gurbin Janar Aliyu Gusau mai ritaya, wanda ya yi murabus a watan jiya.

Najeriya na cigaba da fuskantar matsaloli ta fuskar tsaro.

A ranar Juma'a, watau ranar da Najeriyar ta cika shekara 50 da samun 'yancin kai daga Birtaniya, mutane kimanin 12 sun hallaka a wasu hare haren da aka kai a Abuja, babban birnin Tarayyar kasar.