Abdul jabbar shine shugaban Al Qaeda a Ingila

Mutumin da ake yi wa zargin ta'addanci a Birtaniya, mai suna Abdul Jabbar, wanda aka kashe a watan da ya gabata, ya kasance wani shugaban reshen kungiyar Al Qaeda a Ingila.

Wata majiya daga sama a Pakistan ta shaidawa BBC cewa Abdul Jabbar, wanda aka haifa a Birtaniya, har ma ya auri 'yar can, kafin rasuwarsa na zaune ne a garin Jehlum dake yankin Punjab.

Kimanin watanni ukun da suka gabata ne dai ya kai wata ziyara arewacin Waziristan, wato wurin dake da tsaunuka, a can kusa da kan iyakar Pakistan.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin ya gana da mayakan sa kai kimanin dari uku ko fiye daga kungiyoyin Taliban dana Al Qaeda.

BBC ta samu labarin cewa an nada Abdul Jabbar din ne a matsayin sabon shugaban wani reshe na kungiyar Al Qaeda mai suna Islamic Army of Great Britain.

A lokacin an kuma tattauna shirye shiryen kai hare hare a Birtaniya da Faransa da Jamus, kwatankwacin irin wanda aka kai a birnin Mumbai na kasar India a shekarar 2008.

Sai dai daga majiyar BBC din dake Pakistan har ofishin dake yaki da ta'addanci a Ingila sun jaddada cewa ba'a yi nisa da shirye shiryen kai hare haren ba.