Japan da China zasu kyautata huldar dake tsakaninsu

Firaministan kasar China Wen Jiabao
Image caption Kasashen Japan da China zasu kyautata huldar dake tsakaninsu

A wata ganawa da suka yi a bayan fagen wani taro a Turai, Firaministan Japan, Naoto Kan da takwaransa na kasar China, Wen Jiabao sun jaddada bukatar kyautata hulda tsakanin kasashen biyu.

Wannan dai shi ne karon farko da shugabannin kasashen biyu suka gana tun bayan sabanin diflomasiyya da ya auku tsakanin kasashensu a watan jiya bayan Japan ta tsare wani jirgin ruwa na kamun kifi na 'yan kasar ta China.

Wata sanarwa da ma'aikatar hulda da kasashen wajen Chinan ta fitar tace, shugabannin biyu sun amince su karfafa hulda, kana za su yi wani zama nan gaba.