Hukumar tsaro ta SSS a Najeriya ta sako Raymond Dokpesi

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Hukumomi a Najeriya sun kame shugaban kungiyar yakin neman zaben Janar Ibrahim Badamasi Babangida, inda akai masa tambayoyi sannan kuma aka sako shi

Hukumomi a Najeriya sun kama jagoran yakin neman zaben Janar Ibrahim Babangida, inda aka yi masa tambayoyi, daga bisani kuma aka sako shi, amma aka bukace shi ya mika kansa ga hukumar tsaro ta SSS a yau din nan.

An dai kama Raymond Dokpesi ne dangane da harin bam din da ya hallaka mutane goma sha biyu ranar Juma'ar da ta gabata a Abuja, lokacin da ake bukin cikar Najeriya shekaru hamsin da samun 'yan cin kai.

Masu lura da al'amuran siyasa dai sunyi matukar samun labarin kame Ramond Dokpesi kasancewar yana kusa da shugaba Goodluck Jonathan a da.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin Najeriya sunce an kama shine bisa hujjar wani sakon text da aka gano a wayarsa, wanda ya alakanta shi da Mr. Henry Okah, tsohon jagoran kungiyar MEND, wanda kuma ake zargi yana da hannu a bama baman da suka fashe ranar da najeriya ke bikin cika shekaru hamsin da samun 'yanci