An sake kaiwa Kungiyar Nato hari daga Pakistan

An sake kai hari kan wata tawagar dakarun kungiyar tsaro ta Nato a Pakistan.

Wannan harin dai shi ne na hudu, tun bayan da Pakistan ta rufe babbar hanyar isar da kayayyakin bukatu zuwa kasar Afghanistan a makon jiya.

Rahotanni sun ce 'yan bindiga sun budewa tankokin man fetur wuta a kusa da birnin Quetta da ke iyaka da Afghanistan, in da suka konesu tare da hallaka akalla direba guda.

Mayakan Taliban dai sun ce su ne su ka kai harin, a matsayin martani ga hare- haren da ake kai musu ta hanyar amfani da jiragen sama, wadanda basu da matuka.

Tun makon jiya ne dai tankokin kungiyar tsaro ta Nato ke jibge a Pakistan bayan da aka rufe mashigin Khybar sakamakon wani harin jirgin saman da kungiyar ta kai wanda ya yi ajalin sojin Pakistan uku.