Rashin dorewar manufofi ya mayar da Najeriya baya

Sakamakon wani bincike na nuni da cewa a baya, Najeriya na gaba da kasashe da dama ta fuskar bunkasar tattalin arziki, musamman ma lokacin da kasar ta samu mulkin kai a shekarar 1960.

Binciken ya nuna kasar ta sha gaban wasu kasashe a nahiyar Asiya kamar irinsu Malaysia da Singapore da kuma Saudi Arabia.

Sakamakon binciken na nuni da cewa a baya Najeriyar, itace ke samarwa da kasar Malaysia irin kwakwar manja, abin kuma da ya kasance cikin sahun gaba a bangarorin da kasar ke samun kudaden shigarta.

Amma yanzu wadannan kasashen sun yi wa Najeriyar fintinkau wajen bunkasar tattalin arzikin.

Sai dai kuma masana harkar tattalin arziki a Najeriyar sun bayyana cewa rashin dorewar tsare tsaren tattalin arziki su ne ke yiwa tattalin arzikin kasar illa.

Kowacce gwamnati in ta zo, tana fitowa ne da nata salon, sabanin sauran kasashe.

Sannan kuma wata matsalar itace 'yan Najeriya da dama basa daraja kayan da ake sarrafawa a kasar.