'Yan Najeriya sun sa ido akan sauyin dokokin zabe

Hankulan 'yan Najeriya dai ya karkata ne akan fargabar da wasu 'yan siyasar kasar ke nunawa game da sauye sauyen da majalisar dokokin kasar za ta yi a dokar zabe.

Majalisar dokokin Najeriyar dai za ta fara muhawara ne akan dage lokacin zaben kamar yanda hukumar zabe ta kasa ta bukata.

Tun a watan da ya gabata ne dai, hukumar zaben ta nemi da a kara mata lokaci, domin a ganin ta lokacin da ya yi saura ba zai ishe ta ba.

Sai dai kuma, wasu na fargabar cewa baya ga dage zaben, watakila sabon garambawul din ya hada da sauya yadda jam'iyyu zasu gudanar da zaben fidda gwani, wanda zai bada damar nada dan takarar jam'iyya maimakon zaben cikin gida.

Shugaban kasar Najeriya Dakta Goodluck Jonathan tuni ya gana da shugabannin majalisun dokokin jihohi da gwamnoni akan batun.