Shugaban Senegal ya bawa dansa mukamin minista

Shugabankasar Senegal Abdoulaye Wade
Image caption Shugabankasar Senegal Abdoulaye Wade ya nada dansa, Karim a matsayin ministan makamashin kasar

Shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade ya maye gurbin ministan makamashi na kasar da dansa mai suna Karim, wanda ada can yake rike da wasu manyan mukaman gwamnati.

Shugaba Wade dai ya kori ministan makamashi, Samuel Sarr ne bayan an shafe mako guda al'ummar kasar suna zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da yawan dauke wutar lantarki, musamman ma a babban birnin kasar, Dakar.

A ciki makon na jiya ne dai asusun bada lamuni na duniya, wato IMF yace, karancin wutar lantarki ya zama wata babbar barazana ga tattalin arzikin kasar.