Yawan yaran da suka mutu a Zamfara sakamakon shakar gubar darma ya karu

Hakar ma'adini a Zamfara
Image caption Hakar ma'adini a Zamfara

Majalisar Dinkin Duniya ta yi imanin cewa, akalla kananan yara 400 ne suka mutu a yankin arewacin Najeriya, bayan sun shaki gubar darma.

Majalisar ta ce adadin matattun ya ribanya wanda aka bayar tun farko.

Kungiyar agajin likitocin Faransa ta Medecins Sans Frontieres, ita ce ta bada sabon adadin.

Majalisar Dinkin Duniyar ta aika wata tawagar kai daukin gaggawa, domin ta gudanar da bincike a jahar Zamfara, inda gubar darma ta janyo hasarar rayuka masu yawa, sakamakon hakar zinariya ba bisa ka'ida ba.