Harin NATO: Amruka ta nemi afuwa daga Pakistan

Amurka ta ne mi gafara daga Pakistan game da harin da dakarun NATO suka kai ta Helikwafta a kasar a makon jiya da ya hallaka akalla sojojin Pakistan biyu, lamarin da ya harzika gwamnatin Pakistan. A sanarwar da ta fitar, jakadiyar Amurka a Pakistan, tace jiragen helikwaftan Amurka sun yi tsammanin sojojin da aka kashen 'yan gwagwarmaya ne shi yasa suka bude musu wuta.

Wakiliyar BBC ta ce abu ne mai muhimanci a kare dangantakar dake tsakanin Amurka da Pakistan, sabilida muhimmancin da take da shi wajen yakin da suke a Afghanistan dama kawo karshen ayyukan ta'addanci a Pakistan.