An sabunta: 7 ga Oktoba, 2010 - An wallafa a 16:56 GMT

Shin fasahar intanet ta cancanci lambar yabo ta Nobel?

Fasahar intanet

Fasahar intanet na daga cikin wadanda suke takarar samun lambar yabo ta Nobel kan samar da zaman lafiya a bana.

A ra'ayin masanin falsafa kuma marubuci Farfesa Julian Baggini, bayar da kyautar ta Nobel ga wani abu da ba mutum bane ko wata kungiya, ya dace.

Domin idan ka sanya mutane a wani yanayi da suke zaton babu wanda yake sa musu ido, ga misali aikin dare a gidan yarin Abu Ghuraib na Iraki, za su aikata katobara.

Idan ka sanya su a dai wannan wuri a wani yanayi da suke ganin ana sa ido a kan abinda suke aikata wa, to za su ui aiki bil hakki da gaskiya.

Saboda haka masana falsafa suke ganin, fasahohi ko na'urori da kuma tsari na taimaka wa wajen samar da halayya ta gari daga al'umma.

Cancanta

Ko da hankali zai dauka a baiwa tsari ko wata fasaha lambar yabo ta Nobel, shin fasahar intanet ta cancanci hakan?

Wadanda suka tsayar da fasahar intanet takarar lambar yabon, sun ce "tsarin demokaradiyya na ci gaba ne a duk inda aka samu musayar ra'ayi da muhawaran ta hanyar sadarwa.

Wadanda suka sanya intanet takara sun ce fasahar tana taimaka wa wajen mutane su fito fili su bayyana ra'ayoyinsu ba kumbiya-kumbiya.

Hakan gaskiya ne, sai dai a gani na hakan bai yi kama da fasahar intanet dinda nake amfani da shi a yau da kullum ba.

Ka duba ra'ayoyin da mutane ke bayyana wa a kasan labaran da jaridu ke wallafa wa a intanet, za ka yada mutane ke musayar zazzafar muhawara da cin fuskar juna wanda idan da gaba-da-gaba aka yi hakan ba za a amince da shi ba.

A zahiri fasahar intanet na taimaka wa ne wajen kawo yanayi na hargowa da tayar da jijyar wuya, maimakon fahimtar juna da lumana.

Wani bincike da masani Stanley Milgram ya wallafa, ya nuna cewa mutane na sha'awar su cutar da mutane 'yan uwansu idan ba sa ganinsu.

Ta yiwu a ce wadanda suka tsayar da fasahar intanet takarar lambar yabon sun yi gaskiya da suka ce, tuntubar juna da mutane ke yi ta hanyar fasahar ta intanet na taimaka wa wajen dakushe tsana da kiyayya da ma tashin hankali, sai dai hakan za ta yiwu ne idan an tuntubi junan ne ta hanyar da ta dace.

A fasahar intanet, mutane na komawa suna ne kawai, a don haka mutane kan manta da bukatar mu'amalla da su ta hanyar da ta dace.

Fahimtar juna

Wadanda suka sanya intanet takara sun ce fasahar tana taimaka wa wajen mutane su fito fili su bayyana ra'ayoyinsu ba kumbiya-kumbiya.

Sai dai ba su yi la'akari da yadda wasu mutane ke amfani da ita ba, inda suke alaka da mutane masu ra'ayi irin nasu kawai, maimakon mu'amulla da za ta haifar da fahimtar juna tsakanin bangarori daban daban.

Ta yiwu a ce,fasahar intanet ta sanya abu ne mai wuya a boye gaskiyar al'amari, sai dai a daya bangaren ma ba yadda za a a yi a hana yada karya a cikinta.

Duk da wadannan batutuwan, abu ne da ba za a musanta ba cewa, fasahar intanet na taimaka wa wajen musayar bayanai ta hanyar da ke taimaka wa wajen kawar da jahilci da duhun kai.

Idan muka yi la'akari da wadannan ra'ayoyi mabanbanta, ko za a iya cewa fasahar intanet ta cancanci lambar yabo ta Nobel kan samar da zaman lafiya?

Tuntube mu

* Yana nufin guraben da dole a cike su.

(Kada a zarta bakake dari biyar)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.