Kotun manyan laifuka ta duniya na yiwa alkalan kasashen tsakiyar Afrika bita

Jami'an kotun manyan laifuka ta duniya - ICC na jagorantar wani taro na kara wa wasu alkalan kotunan kasashe takwas na yankin Afrika ta tsakiya, sani kan ayyukan kotun.

Makasudin taron shi ne kara fahimtar da alkalan kotunan kasashen yankin Afrika ta Tsakiya irin bincike-binciken da kotun ke yi a kan wasu manyan jami'an nahiyar Afrika.

A jawabinta wajen taron, mataimakiyar kakakin kotun Fatoumata Dembele Diarra ta ce, kotun kasa da kasar da kotunan kasashen nada manufa iri daya.

Ta ce bukatar kotun ita ce kare mutuncin kotu da kuma tabbatar da hukunta wadanda ake tuhuma da aikata laifuka.