CENI a Niger na taro da IFES kan zabe.

Hukumar zaben Niger na taro tare da IFES
Image caption An fara taron tuntubar juna tsakanin masu ruwa da tsaki kan zabe a Niger

A jamhuriyar Nijar, yau ne hukumar zabe mai cikakken iko - CENI tare da hadin gwiwar wata kungiya ta kasa da kasa wadda ta shahara game da shirya zabuka a duniya - International Fundation for Electoral Systems( IFES) - ta soma wani taron kara wa juna sani na kwanaki 2 wanda ya shafi wasu mambobin hukumar zaben.

Kwararrun masanan da aka gayyata za su yi ma wakilan hukumar zaben cikakkun bayanai kan duk wasu matakan da suka dace a dauka kafin ranar zabe,

Haka kuma taron zai maida hankali game da tsaida ranar zaben, da sauran alamuran na bayan zabe kamar korafe korafe, yayinda a bangare guda kuma, taron zai dubi yadda za a fitar da sakamakon da kowa zai amince da shi ba tare da wata tankiya ba.