Majalisar Nigeria ta yi Allah wadai

Majalisar Nigeria tayi Allah wadai
Image caption Majalisar dattawan Nigeria tayi Allah wadai da harin 1 ga watan October

A Nigeria, majalisar dattawan kasar ta yi wani zama a yau inda tayi Allah wadai da tagwayen hare haren bama baman da aka kai a Abuja babban birnin tarayyar kasar, a ranar 1 ga watan October.

Zaman na majalisar ya wakana ne cikin tsauraran matakan tsaro.

Majalisar ta yi Allah wadai da bam din da aka tayar a ranar daya ga watan Octoba, sannan ta bukaci kwamitocinta da su gudanar da bincike kan lamarin cikin gaggawa.

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin kasar da tayi kokarin hada kan kasa maimakon musayar kalamai tsakanin bangaren gwamnati da wasu yan siyasa da ake zargi suna da hannu a kitsa wannan hari.

Majalisar ta kuma ce za ta yi kokarin hanzarta duba dokar yaki da taaddanci wanda yake gabanta a halin yanzu.

Kungiyar MEND mai fafutukar kwato yancin yankin Niger Delta ce dai ta yi ikirarin kai wannan hari. To amma Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta ikirarin kungiyar, ya na mai cewar wasu yan ta'adda ne daga waje.