Shin ta'addanci na neman mazauni a Najeriya?

Harin bom a Abuja
Image caption Harin bom a Abuja

A yanzu dai Najeriya, wadda ake yi wa daukar babbar yaya a nahiyar Afirka, tana cikin wani hali na tsaka mai wuya, ta fuskar sha'anin tsaro, da siyasa da samun shugabanni na kwarai, da kuma batun dorewar hadin kan al'ummarta da zaman lafiyar ta.

Ganin yadda sha'anin tsaro ya kara sukurkucewa a kasar, kuma aka shiga halin zaman dar-dar da rashin yarda da juna a tsakanin al'ummomi daban-daban na kasar, kungiyoyi da sauran jama'a sun fara bayyana damuwa, tare da laluben kwakkwarar mafita.

Majalisar dattijan Najeriya a nata bangaren na ci gaba da muhawara kan wani kudurin doka kan yaki da ta'addanci.

Wannan mataki dai ya biyo bayan tashin bama-bamai biyu da suka faru a dab da wajen da ake gudanar da bukukuwan cikar kasar shekaru hamsin da samun yancin kanta, a ranar juma'ar da ta gabata, wanda kuma ya janyo asarar rayukan sama da mutane goma da jikkata wasu da dama.

A bayyane take cewa a yanzu batun tsaro shi ne babban abinda ya fi damun jama'ar Nigeria, tun da dai hatta babban birnin kasar kuma dab da inda shugaban kasar wanda ke da daraja ta daya a kasar ma bai tsira daga hare haren bamabamai ba.

Tashin wadannan bama-bamai dai ya zo ne a dai dai lokacin da hukumomin kasar ke kokarin shawo kan matsalar sace-sacen mutane da yin garkuwa da su, da fashi da makami, da riginginmun kabilanci da na addini da suka addabi wasu sassan kasar, abinda hakan ke nuna cewa al'amuran tsaron na kara tabarbarewa wanda wasu ke ganin matukar ba'a dauki matakan da suka kamata ba, lallai lamarin zai kai matsayin da ba za'a iya shawo kansa ba.

Haka kuma rashin tsaron ya kai ga matakin kusan tsayar da al'amura cak a garin Aba dake jahar Abia, inda aka shafe kwanaki bankuna da makarantu a garkame.

Batun hare-haren da 'yan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram ma dai wani babban lamari ne da ya zamewa hukumomin tsaron kasar karfen kafa.

Wani batu kuma da ake ga zai fi duk wadancan barazana ga tsaron kasar shi ne yadda batun tashin bama-baman na makon jiya ke tada jijiyar wuya tsakanin gwamnati da kuma wani sashi na kasar a gefe daya, sannan da kuma wani bangare na wasu da ake ga suna da manufar siyasa da suka ci karo da ta shugaba mai ci a daya bangaren.

Masu lura da al'amura dai na ganin irin wadannan abubuwa na tabarbarewar rashin tsoro na nuni da cewa ta'addanci na neman mazauni a Najeriya, kuma watakila hakan ne ma ya sa majalisar dattijan kasar ta fara mahawara akan kudurin dokar yaki da ta'addanci.

Sai dai mai yiwuwa ne a tafka zazzafar mahawara kan kudurin kafin amincewa da shi ya zama doka, domin wasu na fargabar kada a buge da yin amfani da ita a matsayin karen farauta da za'a ringa razana 'yan bora da shi maimakon yin aiki da ita dan tabbatar da tsaro.