An kai hari ga yan kasashen waje a Yemen

An kai hari a Yemen
Image caption An kashe wani Bafaranshe a Yemen.

An kashe wani Bafaranshe sannan kuma an jikkata wasu Yan Birtaniya 2 a wasu hare hare da aka kai daban-daban a Sana'a babban birnin kasar Yemen.

An hari wata motar Diplomasiya dake kan hanyarta ta zuwa Ofishin jakadancin Birtaniya, jim kadan kafin wani harbi a wani kamfanin mai da iskar gas.

Hare haren sun zo ne yan kwanaki bayanda hukumomin Yemen sun yi gargadi game da karuwar hadari daga yan gwagwarmayar kungiyar Al-Qa'ida a babban birnin.

Idan ba a manta ba, a farkon wannan shekarar, an yi yunkurin hallaka jakadan Birtaniya a kasar ta Yemen.