Amurka ta yi wani bincike akan yunkurin Pakistan

Sakamakon wani bincike da fadar gwamnatin Amurka tayi akan kudurin Pakistan na daukar matakin kawo karshen mayakan sa kai dake arewacin Waziristan, gab da iyakarsu da Afghanistan, na nuni da wani yanayi mai sarkakiya.

Sannan kuma akwai shakku akan shugaban kasar Pakistan din wanda farin jininsa ke kara dusashewa.

Bincike na baya baya da fadar white house ta yi game da fadan da ake yi a Afghanistan, na nuni da cewa a bisa dalilai masu yawa, sojin Pakistan sun ki daukar mataki akan kungiyoyin Taliban dana Al Qaeda dake iyakar kasar.

Rahoton dai na nuni da karancin kayan aikin da sojin Pakistan din ke fuskanta, wanda hakan ya sanya suke zabar abinda zasu iya yi, su bar wanda ba zasu iya ba.

Bugu da kari, ambaliyar ruwan da ta far wa kasar ba karamin tashin hankali ta janyo wa jami'an pakistan din ba.

Sai dai kuma binciken na nuni da cewa sojin na aiki ne kawai a kusa da kan hanyoyi, wanda hakan ke baiwa mayakan sa kan da aka rarako damar samun mazaunin yada zango.

Rahoton dai ya kalubalanci shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari da yin bulaguro zuwa nahiyar turai a lokacin da ambaliyar ruwa ta mamaye kasarsa a watan Agustar daya gabata.

Rahoton ya ce wannan ba karamar illa ya yiwa kimarsa a gida da waje ba.