Fursunoni sun yi bore a Bauchi

A jihar Bauchi ta arewacin Najeriya wasu fursunoni sun yi bore inda suka cinnawa wani bangare na gidan yarin wuta.

Bayanai dai na nuna cewa sun yi wannan bore ne saboda abinda suka yi zargin rashin adalci ne daga bangaren gwamnatin jihar Bauchi.

Fursunonin masu bore sun yi zargin cewargwamnatin ta yiwa wasu fursunoni takwarorinsu afuwa, su kuma a cewarsu aka barsu.