Ana cikin fargaba a Borno

A jihar Borno dake arewacin Najeriya, ana ci gaba da alhinin kisan gillar da yan bindiga suka yiwa mataimakin shugaban jam'iyar ANPP na kasa shiyyar arewa maso gabacin Najeriya, Alhaji Awana Ngala a daren jiya.

Jama'a da dama na ci gaba da nuna fargaba game da irin wadannan jerin hare hare da aka shafe watanni ana kaiwa kan jami'an yan sanda da masu unguwanni birnin Maiduguri.

Haka nan kuma jama'a da dama na nuna shakku a kan irin matakan tsaron da gwamnatin ke cewa ta dauka na shawo kan wannan matsala.

Ana zargin cewa yan kungiyar Boko Haram ne suke kai wadannan hare hare.