Kongo ta kai hari kan 'yan kabilar Hutu

Rundunar sojan jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo ta ce ta kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan 'yan tawayen kabilar Hutu a gabashin kasar.

Wani mai magana da yawun sojan ya shaidawa BBC cewa an tura bataliya shida ta sojoji zuwa lardin Kivu ta Arewa, domin yin abin da ya kira, gamawa da 'yan tawayen.

Wata kungiya mai mara baya ga 'yan tawayen ta zaegi dakarun gwamnatin da kai hare hare a kan fararen hula a yankin. A 'yan shekarun da suka wuce, yankin Kivu ta Arewa ya yi fama da rigingimu; kuma jerin yunkurin da aka yi a baya na murkushe 'yan tawayen kabilar Hutun, wadanda wasunsu ke da hannu a kisan kare dangin Rwanda na 1994, bai samu nasara.