IMF ta yi gargadi kan yiwuwar rikici tsakanin China da Kasashen Yamma

Shugaban Asusun bada lamuni na duniya, IMF, Dominique Strauss-Kahn, yayi gargadi kan hadarin abin da ya kira yakin takardar kudi, da ka iya barkewa tsakanin kasar Sin da kasashen yammacin duniya.

Amurka na korafin cewa an karya darajar takardar kudin kasar ta Sin wato Yuan.

Mr Strauss-Kahn, ya ce rashin daidaito a farfadowar tattalin arziki na daga cikin abin da ke janyo ana yi wa juna kallon hadarin kaji;

Ya ce, a fili take cewa tattalin arzikin na farfadowa, amma kamar yadda kowa ya sani, farfadowar ba mai karfi ba ce. Kuma ta wani bangaren, rashin karfin, na faruwa a sakamakon rashin daidaito.

Lokacin da yake magana Brussels jiya, Praministan kasar Sin Wen Jiabao ya ce idan aka kara darajar kudin kasar tashi guda, lamarin zai sa Sinawa rasa aiki,da kuma janyo tarzoma.