An shirya wani taron hadin guiwa a Kaduna kan matsalolin zabe a Najeriya

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta a Najeriya wato INEC tare da hadin gwiwar kungiyar bada tallafi ta Amurka --USAID sun shirya wani taro na tuntubar juna tsakanin hukumar ta zabe da kuma shugabannin jamiyyu a wasu jihohin arewacin kasar a Kaduna.

An shirya taron ne don duba matsalolin da suka addabi zabe a kasar da kuma ganin yadda za a kawo karshensu a zaben 2011 dake tafe.

'Yan siyasa daga jihohin kwara, da Neja da Abuja da kuma Kaduna ne dai suka halarci wannan taro.