Kenya ta kori malamai kusan dubu daya

An kori malamai dubu a Kenya
Image caption An kori malamai dubu a Kenya

Gwamnatin kasar Kenya ta ce malaman makaranta kimanin dubu daya ne aka kora daga aiki cikin shekaru biyunda suka gabata, bisa laifin yin lalata da dalibai 'yan mata.

Ahmed Hussain na sashen kula da walwalar kananan yara a Kenya ya shaidawa BBC cewa, ba su tantance tsawon lokacin da aka kwashe ana cin zarafin kananan yaran ba, amma an daure wasu daga cikin malaman.

Ya ce an kai da dama daga cikinsu kotu, an kuma daure su. Wasunsu lokacinda lamarin ya fito fili an dauki mataki kansu.

Mr Hussain ya ce wani layin wayar tarho na da aka bude, domin agaza wa wadanda lamarin ya shafa, ya sa an fahimci cewar matsalar ta fi yadda aka zata, kamari.