An sace wani jami'in majalisar dinkin duniya

Rahotanni na bayyana cewa an sace wani jami'in kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya UNAMID a Darfur.

Lamarin dai ya faru ne a garin El Fasher, inda kwamitin ya kai ziyara a wani rangadi na kwanaki hudu da ya ke yi a Sudan. Kamar dai yanda dakarun wanzar da tsaro suka bayyana, wadansu dauke da makamai sun kutsa kai ne cikin gidan da jami'an kungiyar su hudu suke.

An daure biyu daga cikin mutanen, yayin kuma da aka yi awan gaba da biyu.

Daya dai ya yi nasarar tserowa, amma har yanzu dayan ba a ji duriyarsa ba.

Sace sacen mutane sun kara yawaita a kasar tun bayan da kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayar da izinin cafke shugaba Omar Al Bashir.

Kuma ana yin mafi yawan sace sacen ne da zummar neman kudin fansa.

Sai dai kuma lokacin da wannan lamarin ya afku, da kuma garin da dakarun wanzar da tsaro na majalisar dinkin duniya su ke, abu ne da kwamitin zai damu dashi.

Dama dai mambobin kwamitin ba su samu kyakkyawar tarba daga magoya bayan shugaba Al Bashir ba.

Sannan ma akwai labarin barkewar rikici a wadansu wuraren a yankin Darfur.

Yanzu dai hankali ya karkata ne akan kuri'ar raba gardamar da za'a kada a watan junairu mai zuwa wadda za ta baiwa kudancin kasar cin gashin kanta.