'Yan siyasa na cece-kuce kan sayan jirgi a Ghana

Shugaban Ghana
Image caption Shugaban Ghana

'Yan siyasa a Ghana suna zargin gwamnati da yin baki biyu bayan da ta kaddamar da wani sabon jirgin saman shugaban kasa, 'yan watani bayan da suka yi yunkurin hana sayen jirgin, lokacin da suke 'yan adawa.

Wani tsohon ministanm cikin gida, Nana Obiri Boahen ya nuna mamaki kan yadda aka kaddamar da sabon jirgin saman, yana mai zargin shugaban kasar, John Atta Mills da jam'iyyarsa da aikata rashin gaskiya.

Gwamnatin Ghana dai ta ce jirgin saman wanda kudinsa dala miliyan talatin ne, zai baiwa jami'an gwamnati damar yin tafiye tafiye cikin mutunci, da kuma tsaron lafiya.

Jirgin saman sampurin Dasault Falcon kirar kasar Faransa shi ne ya maye gurbin wanda ake amfani da shi mai shekaru talatin.