An kashe gwamnan lardin Kunduz a Afghanistan

A Afghanistan, gwamnan lardin Kunduz na arewacin kasar, Mohammad Omar ya rasa ransa, a sakamakon fashewar wani bam a wani masallaci a lardin Takhar dake makwabtaka da su.

Wasu mutanen akalla su goma sha hudu sun mutu a harin bam din, wanda aka kai lokacin sallar Juma'a. Akwai wasu karin mutanen da suka jikkata.

Wakilin BBC ya ce babu watakungiya da ta ce ita ta kai karin, amma dai yan Taliban da kuma kungiyar Islama ta Uzbekistan duka suna kai hare hare a yankin.

Gwamnan Takhar , ya ce an kai harin ne a kan takwaran aikin nasa. Ya ce Muhammad Omar ya saba yin sallar Juma'a a masallacin, kuma sau uku, a baya, yana tsallake rijiya da baya, a yunkurin halaka shi.