Palasdinawa na neman goyan baya don janyewa daga shawarwari

Amr Mousa
Image caption Amr Mousa

Shugaban kungiyar kasashen Larabawa Amr Musa ya bada bayanai marasa karfafa gwiwa kan dorewar tattaunawar sulhu tsakanin Isra'ila da Palasdinawa.

Mr Amr Musa, ya ce halin da ake ciki, ba mai dadin ji ba ne, kuma bai dace da tattaunawar gaba da gaba ba.

Amr Musa ya bayyana haka ne a garin Sirte, na gabar teku a Libya, gabanin jawabin da jagoran Palasdinawa Mahmud Abbas zai yi ga ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa.

Ana sa ran Mahmud Abbas zai nemi goyon bayan kasashen Larabawa domin kawo karshen tattaunawar, sakamakon yadda Isra'ila ta ki dakatar da gina matsugunan Yahudawa a gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye.