Shugaba Obama ya nemi Sin ta sako Liu Xiaobo

Mr Liu Xiaobo
Image caption Mr Liu Xiaobo

Shugaba Barrak Obama ya yi kira ga kasar Sin da ta sako, mutumin nan mai nuna bijirewar da ta daure Liu Xiaobo, ba tare da bata lokaci ba.

A yau ne aka bayyana Mr Liu Xiaobo a matsayin wanda aka baiwa kyautar yabo ta Noble ta zaman lafiya.

Gwamnatin kasar Sin dai ta maida martani a fusace game da kyautar, tana mai cewar Mr Liu, mai laifi ne.

Kakakin gwamnatin kasar Sin ta ce mutumin da ake magana a kansa, kotun kasar Sin ta daure shi, saboda ya karya dokar kasarta. Abin da ya aikata ya saba ma manufar bada kyautar Nobel ta zaman lafiya.

A watan Disamba ne aka yankewa Mr Liu Xiaobo hukuncin daurin shekaru sha daya, bayan wallafa wata kasida dake kiran da a aiwatar da sauye sauyen siyasa a kasar ta Sin.