Mutane sun halaka a Bangladesh

Wuraren da ruwan sama ya shafa
Image caption Mutane sun halaka sakamakon ruwan sama a Bangladesh

Kimanin mutane goma sha biyar ne suka halaka yayin da wasu da dama suka bace ranar asabar a Bangladesh, sakamakon ruwan saman da a ka tafka.

Rahotanni sun ce mutane dubu dari biyar ne kuma suka rasa muhallansu.

A kudancin kasar, fiye da kauyuka saba'in ne ruwan saman ya mamaye hade da gonaki da dabbobi.

An kwashen kwanaki da dama ana yin ruwa kamar-da-bakin-kwarya a kasar.