Hukuncin kotu akan Misis Cecelia Ibru

Babban bankin Najeriya, CBN ya bayyana hukuncin daurin wata shida a gidan yari, da wata babbar kotu da ke Jihar Lagos ta yankewa tsohuwar shugabar bankin Oceanic, Misis Cecelia Ibru a matsayin babban cigaba.

An kuma umarci Misis Ibru da ta biya fiye da dalar Amurka biliyan guda a sanadiyyar aikata laifin almundahana.

Misis Cecelia Ibru dai ta amince da aikata laifuffuka uku daga cikin laifuka ashirin da bakwai da hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati ke tuhumarta akai.

A bara ne babban bankin Najeriyar ya fitar da wani rahoto da ke bayyana cewa wadansu shugabannin bankuna a kasar na dab da durkusar da bankunan da suke shugabanta.

Misis Cecilia Ibru na daya daga cikin shugabannin bankunan da aka kama a bara.

Mutane da dama dai sun yi mamakin wannan hukuncin, ganin yanda ya kan yi wuya a yankewa manyan 'yan kasuwa ko kuma 'yan siyasa hukuncin dauri.